16 Satumba 2020 - 15:28
​Libya: Firayi Ministan Gwamnatin Tripoli Zai Yi Murabus A Yau

Firayi ministan gwamnatin Tripoli Fa’iz Suraj zai sanar da yin murabus a yau, tare da bayyana dalilansa na daukar wannan mataki ta hanyar jawabin da zai gabatar wanda gidan talabijin na kasar zai watsa kai tsaye.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayar da rahoton cewa, Suraj zai yi murabus a yau Laraba a jawabin da zai gabatar wanda gidan talabijin na Libya zai watsa daga birnin Tripoli.

Rahoton ya ce wannan yana a matsayin sharer fage ne na cimma daidaito taskanin bangarorin siyasar kasar Libya, domin kawo karshen rikicin da kasar take ciki.

A jiya Talata ne dai firayi ministan gwamnatin Bengazi da ke biyayya ga janar Khalifa Haftar ya sanar da yin murabus, inda dukkanin bangarorin biyu za su ci gaba da daukar matakai da za su kai ga kafa gwamnatin hadin kansa, wadda za ta hada dukkanin bangarorin siyasar kasar.

A cikin wannan makon ne dai aka gudanar da zaman tattaunawa a kasar Switzerkand karkashin kulawar majalisar dinkin duniya, zaman da ya hada bangarorin siyasa da ba su ga maciji da juna a kasar Libya.

Nan da watanni 18 masu zuwa ne ake sa ran za a gudanar da zaben ‘yan majalisa wanda dukkanin bangarori za su shiga, daga karshe kuma a kafa gwamnatin hadin kasa.

342/